7 Kada kuma su ƙara yin hadayunsu ga gumaka masu siffar bunsurai waɗanda suka bauta wa. Wannan doka ce ta har abada a gare su har dukan zamanansu.
8 Kowane Ba'isra'ile, ko baƙon da yake baƙunta a cikinsu, wanda ya miƙa hadaya ta ƙonawa ko sadaka,
9 amma bai kawo ta a ƙofar alfarwa ta sujada, ya miƙa ta ga Ubangiji ba, sai a fitar da wannan mutum daga cikin jama'a.
10 Idan wani Ba'isra'ile, ko baƙon da yake baƙunta a cikinsu ya ci jini, Ubangiji zai yi gāba da wannan mutum da ya ci jinin ya fitar da shi daga cikin jama'a.
11 Gama ran nama yana cikin jinin, Ubangiji kuwa ya ba su shi a bisa bagade domin a yi wa rayukansu kafara, gama da jini ake kafara saboda akwai rai a cikinsa.
12 Saboda haka Ubangiji ya faɗa wa mutanen Isra'ila, cewa, kada wani daga cikinsu, ko baƙon da yake baƙunta a cikinsu, ya ci jini.
13 Idan kowane Ba'isra'ile, ko baƙon da yake baƙunta a cikinsu ya tafi farauta, ya kama nama, ko tsuntsu da ake ci, sai ya zub da jininsa, ya rufe da ƙasa.