1 Ubangiji ya ce wa Musa
2 ya faɗa wa dukan taron jama'ar Isra'ila cewa, “Ku zama tsarkakakku, gama ni Ubangiji Allahnku mai tsarki ne.
3 Sai ko wannenku ya girmama mahaifiyarsa da mahaifinsa, ya kuma kiyaye lokatan sujada. Ni ne Ubangiji Allahnku.
4 “Kada ku juya ku bi gumaka, ko kuma ku yi wa kanku gumaka na zubi. Ni ne Ubangiji Allahnku.