15 Za su ƙidaya mako bakwai daga kashegarin Asabar da suka kawo damin hadaya ta kaɗawa domin miƙa wa Ubangiji.
16 Kwana hamsin za su ƙirga zuwa kashegarin Asabar ta bakwai ɗin. Sa'an nan sai su kawo hadaya ta sabon hatsi ga Ubangiji.
17 Za su kawo malmala biyu na abinci da za a kaɗa daga inda suke domin a miƙa su ga Ubangiji. Za a yi malmalan da rabin garwar gari mai laushi. Za a sa wa garin yisti, sa'an nan a toya. Hadaya ta 'ya'yan fari ke nan ga Ubangiji.
18 Za su kuma miƙa 'yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya marasa lahani, da bijimi ɗaya, da raguna biyu tare da abincin. Za a yi hadaya ta ƙonawa da su ga Ubangiji, tare da hadayarsu ta gari, da hadayarsu ta sha, wato, hadaya ta ƙonawa da wuta, hadaya ce mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
19 Za su miƙa hadaya ta zunubi da bunsuru ɗaya, da 'yan raguna biyu bana ɗaya ɗaya don hadaya ta salama.
20 Firist zai kaɗa su tare da abinci na nunan fari domin hadaya ta kaɗawa, da 'yan ragunan nan biyu a gaban Ubangiji. Za su zama tsarkakakku ga Ubangiji domin a ba firist.
21 A ranar fa za su yi shela don a yi muhimmin taro. Ba za su yi aiki mai wuya ba. Wannan doka ce gare su har abada a inda suke duka.