1 Ubangiji kuwa ya yi wa Musa magana a kan Dutsen Sina'i, ya ce
2 ya faɗa wa Isra'ilawa ka'idodin nan. Sa'ad da suka shiga ƙasar da Ubangiji yake ba su, ƙasar za ta kiyaye shekara ta bakwai ga Ubangiji.
3 Shekara shida za su yi, suna ta noman gonakinsu, suna kuma ta aske gonakin inabinsu, suna tattara amfaninsu.
4 Amma shekara ta bakwai ta Ubangiji ce, sh ekara ce ta hutawa ga ƙasar. Kada su nomi gonakinsu, ko kuwa su aske inabinsu.
5 Kada su girbe gyauron gonakinsu da na inabin da ba su yi wa aski ba. Za ta zama shekarar hutawa ta musamman ga ƙasar.