5 Za ku yi ta girbi, har lokacin tattara 'ya'yan inabi, za ku kuma yi ta tattara 'ya'yan inabi har zuwa lokacin shuka. Za ku ci abincinku, ku ƙoshi, ku yi zamanku a ƙasarku lafiya.
6 “Zan ba da salama cikin ƙasar. Za ku kwanta, ba abin da zai razana ku. Zan kawar da mugayen dabbobi daga ƙasar. Ba za a ƙara yin yaƙi a ƙasarku ba.
7 Za ku runtumi maƙiyanku, za su kuwa fāɗi ta kaifin takobi a gabanku.
8 Mutum biyar ɗinku za su runtumi mutum ɗari, mutum ɗari ɗinku za su runtumi mutum dubu goma. Maƙiyanku kuwa za su fāɗi a gabanku ta kaifin takobi.
9 Zan dube ku da idon rahama, in sa muku albarka, in riɓaɓɓanya ku. Zan tabbatar muku da alkawarina.
10 Za ku girbi amfani mai yawa har kun zubar da sūnā tukuna kafin ku sami wurin ajiye sabo.
11 Zan kafa wurin zamana a tsakiyarku, ba kuwa zan gaji da ku ba.