14 Sa'an nan mai hadayar zai ba da kitsen da yake rufe da kayan cikin, da wanda yake bisansa,
15 da ƙodoji biyu, da kitsen da yake bisansu wajen kwiɓi, da matsarmama don a miƙa su hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji.
16 Firist kuwa zai ƙone su a bisa bagaden kamar hadayar abincin da akan ƙone don ya yi ƙanshi mai daɗi. Dukan kitse na Ubangiji ne.
17 Ba za a ci kitse ko jinin ba a wuraren zamanku. Wannan doka madawwamiya ce.