5 In mutum ya aikata ɗaya daga cikin waɗannan laifofi, sai ya hurta laifin da ya yi.
6 Ya kuma kawo hadaya ga Ubangiji don laifin da ya yi. Sai ya kawo 'yar tunkiya ko akuya domin hadaya don zunubi. Firist zai yi kafara don laifin mutumin.
7 Amma idan 'yar tunkiyar ta fi ƙarfinsa, sai ya kawo kurciyoyi biyu ko 'yan tattabarai biyu don yin hadaya ga Ubangiji saboda laifin da ya yi. Ɗaya za ta zama ta yin hadaya don laifi, ɗayan kuwa don yin hadaya ta ƙonawa.
8 Zai kawo su wurin firist. Da fari firist zai miƙa hadaya don laifi. Zai karye wuyanta, amma ba zai tsinke kan ba.
9 Zai yayyafa jinin hadaya don laifi a gefen bagaden, sauran jinin kuwa zai tsiyaye a gindin bagade, gama hadaya ce don laifi.
10 Sa'an nan zai miƙa ta biyun don hadaya ta ƙonawa bisa ga yadda aka ƙayyade. Firist ɗin zai yi kafara saboda laifin da mutumin ya yi, za a kuwa gafarta masa.
11 Amma idan har kurciyoyi biyu, ko 'yan tattabarai biyu sun fi ƙarfinsa don yin hadaya saboda laifinsa, sai ya kawo humushin garwar gari mai laushi don yin hadaya saboda laifinsa. Ba zai zuba mai ko lubban a garin ba, gama hadaya ce don laifi.