22 Wanda aka keɓe daga zuriyar Haruna, shi ne zai miƙa wannan hadaya ga Ubangiji. Za a ƙone ta duka. Wannan farilla ce har abada.
23 Kowace hadaya ta gari ta firist, za a ƙone ta ɗungum, ba za a ci ba.
24 Sai Ubangiji ya umarci Musa
25 ya ba Haruna da 'ya'yansa maza waɗannan ka'idodi domin hadaya don zunubi. A inda ake yanka hadaya ta ƙonawa, a nan ne za a yanka hadaya don zunubi a gaban Ubangiji, hadaya ce mai tsarki.
26 Firist wanda ya miƙa hadaya don zunubi zai ci daga ciki a wuri mai tsarki a cikin farfajiyar alfarwa ta sujada.
27 Duk wanda ya taɓa naman zai tsarkaka, in kuma jinin ya ɗiga a riga, sai a wanke rigar a wuri mai tsarki.
28 Sai a fasa tukunyar ƙasa wadda aka dafa naman a ciki, amma in a cikin tukunyar tagulla aka dafa, sai a kankare ta a ɗauraye da ruwa.