5 Firist zai ƙone su a bisa bagaden, gama hadaya ce da akan ƙone da wuta ga Ubangiji, hadaya ce don laifi.
6 Kowane namiji a cikin firistoci zai iya ci. Sai a wuri mai tsarki za a ci, gama tsattsarkan abu ne.
7 Hadaya don laifi kamar hadaya don zunubi take, saboda haka ka'idar yinsu iri ɗaya ce. Firist wanda ya yi kafarar, zai ɗauki abin da ya ragu.
8 Firist kuma wanda ya miƙa hadaya ta ƙonawa ta wani mutum, zai ɗauki fatar abin da aka yi hadayar da shi.
9 Kowace hadaya ta gari da aka toya cikin tanda, da duk wadda aka yi a tukunya ko a kaskon tuya, za su zama na firist wanda ya miƙa hadaya.
10 Kowace hadaya ta gari kuma wadda aka kwaɓa da mai, ko wadda ba a kwaɓa ba, za ta zama rabon 'ya'yan Haruna, maza duka, kowa da kowa.
11 Waɗannan su ne ka'idodin hadaya ta salama wadda za a miƙa wa Ubangiji.