1 Yefta mutumin Gileyad ne, shi kuwa jarumi ne, amma mahaifiyarsa karuwa ce. Gileyad ne mahaifinsa.
2 Matar Gileyad ta haifa masa 'ya'ya maza. Sa'ad da suka yi girma, sai suka kori Yefta, suka ce masa, “Ba za ka ci gādo a gidan mahaifinmu ba, gama kai ɗan wata mace ne.”
3 Sai Yefta ya gudu daga wurin 'yan'uwansa, ya zauna a ƙasar Tob. 'Yan iska kuwa suka taru wurin Yefta, sukan tafi yawo tare da shi.
4 Ana nan sai Ammonawa suka kai wa Isra'ilawa yaƙi.
5 Da haka ta auku, sai shugabannin Gileyad suka tafi su komo da Yefta daga ƙasar Tob.
6 Suka ce wa Yefta, “Ka zo, ka zama shugabanmu don mu yi yaƙi da Ammonawa.”