L. Mah 6 HAU

Kiran Gidiyon

1 Jama'ar Isra'ila kuma suka sāke yin zunubi a gaban Ubangiji, sai Ubangiji ya ba da su ga Madayanawa su mallake su shekara bakwai.

2 Madayanawa kuwa sun fi Isra'ilawa ƙarfi, saboda haka Isra'ilawa suka yi ta ɓuya a kogon dutse, da waɗansu wuraren ɓuya a tsaunuka.

3 Duk lokacin da Isra'ilawa suka yi shuka, sai Madayanawa, da Amalekawa, da waɗansu kabilai na hamada su zo su fāɗa musu.

4 Sukan zo su kafa musu sansani, su ɓaɓɓata amfanin ƙasar har zuwa kusa da Gaza. Ba su barin wani abinci a ƙasar Isra'ila, domin Isra'ilawa ko dabbobinsu.

5 Gama sukan zo da dabbobinsu da alfarwansu da yawa, kamar fara. Su da raƙumansu ba su ƙidayuwa, sukan zo, su lalatar da ƙasar.

6 Isra'ilawa suka sha ƙasƙanci ƙwarai a hannun Madayanawa. Sai suka yi kuka ga Ubangiji domin ya taimake su.

7 Da Isra'ilawa suka yi kuka ga Ubangiji saboda wahalar da Madayanawa suke ba su,

8 sai Ubangiji ya aika musu da wanda ya faɗa musu saƙon Ubangiji, Allah na Isra'ila, ya ce, “Ni ne na fito da ku daga bauta a Masar.

9 Na cece ku daga Masarawa, da kuma waɗanda suka yi yaƙi da ku a nan. Na kore su a gabanku, na ba ku ƙasarsu.

10 Na faɗa muku, ‘Ni ne Ubangiji Allahnku, kada ku bauta wa gumakan Amoriyawa, waɗanda kuke zaune a ƙasarsu.’ Amma ba ku yi biyayya da maganata ba.”

11 Mala'ikan Ubangiji ya zo, ya zauna a gindin itacen oak na Yowash mutumin Abiyezer, a ƙauyen Ofra. Ɗansa Gidiyon kuwa yana susukar alkama daga ɓoye, a wurin da ake matse ruwan inabi, don ya ɓuya daga Madayanawa.

12 Mala'ikan Ubangiji kuwa ya bayyana gare shi, ya ce, “Kai jarumi ne, Ubangiji kuma yana tare da kai.”

13 Sai Gidiyon ya ce masa, “Ya shugabana, idan Ubangiji yana tare da mu, me ya sa abubuwan nan suka same mu? Ina kuma ayyukansa masu ban al'ajabi waɗanda kakanninmu suka faɗa mana cewa, ‘Ai, Ubangiji ne ya fisshe mu daga Masar’? Amma yanzu Ubangiji ya yi watsi da mu, ya ba da mu ga Madayanawa.”

14 Ubangiji ya ce masa, “Tafi da dukan ƙarfinka, ka ceci Isra'ilawa daga Madayanawa. Ni kaina na aike ka.”

15 Gidiyon ya amsa ya ce, “Ubangiji, yaya zan yi in ceci Isra'ilawa? Ga shi, dangina ne mafi ƙanƙanta a kabilar Manassa, ni ne kuma ƙarami a gidanmu.”

16 Ubangiji kuwa ya ce masa, “Za ka iya, gama zan taimake ka. Za ka muttsuke Madayanawa kamar mutum guda.”

17 Gidiyon kuwa ya ce masa, “Idan ka amince da ni, ka nuna mini alama don in sani kai kake magana da ni.

18 Ina roƙonka, kada ka tashi daga nan, sai na kawo maka hadaya ta abinci.”Ya amsa cewa, “Zan tsaya har ka kawo.”

19 Gidiyon ya tafi gida, ya yanka ɗan akuya, ya dafa, ya yi waina marar yisti ta gāri mudu guda. Ya sa naman a kwandon, romon kuwa ya zuba a tukunya, ya kawo, ya miƙa masa a gindin itacen oak.

20 Mala'ikan Allah kuma ya ce masa, “Ɗauki naman da wainar marar yisti ka sa a kan dutsen nan, sa'an nan ka zuba romon a kai.” Haka kuwa ya yi.

21 Mala'ikan Ubangiji kuwa ya miƙa kan sandan da yake hannunsa, ya taɓa naman da wainar, sai wuta ta fito daga dutsen ta cinye naman da wainar. Mala'ikan Ubangiji kuwa ya ɓace masa.

22 Da Gidiyon ya gane mala'ikan Ubangiji ne, sai ya ce, “Kaitona, Ubangiji Allah, gama na ga mala'ikan Ubangiji fuska da fuska.”

23 Amma Ubangiji ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, ba za ka mutu ba.”

24 Gidiyon kuwa ya gina wa Ubangiji bagade a wurin, ya sa masa suna, Ubangiji Salama Ne. Har wa yau bagaden yana nan a Ofra, ta iyalin Abiyezer.

25 A wannan dare Ubangiji ya ce masa, “Ka ɗauki bijimin mahaifinka, da wani bijimin bana bakwai. Sa'an nan ka rushe bagaden gunkin nan Ba'al na mahaifinka, ka sare gumakan da suke kusa da shi.

26 Sa'an nan ka gina wa Ubangiji Allahnka bagade mai kyau a kan wannan kagara. Ka ɗauki bijimi na biyu ka miƙa shi hadayar ƙonawa da itacen gumakan da za ka sare.”

27 Gidiyon fa ya ɗauki mutum goma daga cikin barorinsa, ya yi yadda Ubangiji ya faɗa masa. Amma domin yana tsoron, mutanen gidansa da na gari, bai yi wannan da rana ba, sai da dare.

28 Da mutanen garin suka tashi da safe, sai ga bagaden Ba'al a farfashe, gumakan kuma da suke kusa da shi, an sare. Bijimi na biyu kuma, an miƙa shi hadaya a kan bagaden da aka gina.

29 Suka ce wa juna, “Wa ya yi wannan abu?” Da suka binbincika, sai suka tarar Gidiyon ne, ɗan Yowash, ya yi shi.

30 Sai suka ce wa Yowash, “Ka kawo ɗanka a kashe, gama ya rushe bagaden gunkin nan Ba'al, ya kuma sare gumakan da suke kusa da shi.”

31 Yowash kuwa ya ce wa dukan waɗanda suka tasar masa, “Za ku yi hamayya domin gunkin nan Ba'al, ko kuwa za ku goyi bayansa? Duk wanda ya yi hamayya dominsa za a kashe shi da safe. Idan shi allah ne, to, bari ya yi hamayya don kansa, gama an farfashe bagadensa.”

32 A ranar nan aka laƙaba wa Gidiyon suna Yerubba'al, wato “Bari gunki Ba'al ya yi hamayya don kansa, domin an farfashe bagadensa.”

33 Dukan Madayanawa kuwa, da Amalekawa, da mutanen gabas suka tattaru. Suka haye, suke kafa sansaninsu a kwarin Yezreyel.

34 Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko a kan Gidiyon, sai ya busa ƙaho, mutanen Abiyezer suka bi shi.

35 Ya kuma aiki manzanni a ƙasar Manassa duka. Su kuma aka kirawo su su bi shi. Ya kuma aiki manzanni zuwa ga Ashirawa da Zabalunawa, da Naftaliyawa, su kuma suka zo, suka haɗa kai da shi.

36 Sa'an nan Gidiyon ya ce wa Allah, “Ka ce za ka sa ni in ceci Isra'ilawa.

37 To, zan shimfiɗa ulu a masussuka. Idan da safe akwai raɓa a kan ulun kaɗai, ƙasa kuwa a bushe, sa'an nan zan sani za ka ceci Isra'ilawa ta hannuna kamar yadda ka faɗa.”

38 Haka kuwa ya zama Kashegari Gidiyon ya tashi da sassafe, sai ya matse ulun, ruwan raɓa da ya matse daga ulun kuwa, ya cika ƙwarya.

39 Gidiyon kuma ya ce wa Allah, “Ina roƙonka, kada ka yi fushi da ni, bari in ƙara magana sau ɗaya kurum, wato in sāke yin gwaji da ulun. Ina roƙonka ka sa a yi raɓa a ƙasa, amma kada ta taɓa ulun.”

40 Haka kuwa Allah ya yi a daren. Aka yi raɓa a ƙasa, amma ulun yana a bushe.

Surori

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21