1 A wannan rana Debora da Barak, ɗan Abinowam, suka raira wannan waka,
2 Yabo ya tabbata ga Ubangiji!Isra'ilawa suka ƙudura su yi yaƙi.Mutane suka sa kansu da farin ciki.Alhamdu lillahi!
3 Ku kasa kunnenku ya ku sarakuna,Ku lura, ya ku hakimai,Zan raira waƙa in yi kaɗe-kaɗe ga Ubangiji,Allah na Isra'ila.
4 Ya Ubangiji, sa'ad da ka bar duwatsun Seyir,Sa'ad da ka fito daga jihar Edom,Ƙasa ta girgiza,Ruwan sama ya zubo daga sararin sama,I, gizagizai suka kwararo da ruwa.
5 Duwatsu suka girgiza a gaban Ubangijin Sina'i,A gaban Ubangiji, Allah na Isra'ila.