3 Sai dangin mahaifiyarsa suka yi magana da shugabannin Shekem saboda shi. Zuciyarsu kuwa ta saje da Abimelek, gama suka ce, “Shi ɗan'uwanmu ne.”
4 Suka kuma ba shi azurfa saba'in daga cikin gidan gunkin nan Ba'al-berit. Da wannan azurfa Abimelek ya yi ijarar 'yan iska waɗanda suka bi shi.
5 Ya tafi gidan mahaifinsa a Ofra, ya kashe 'yan'uwansa maza, wato 'ya'yan Yerubba'al, mutum saba'in a kan dutse guda. Amma Yotam ƙaramin ɗan Yerubba'al, shi kaɗai ya ragu domin ya ɓuya.
6 Sai shugabannin Shekem duka da na Betmillo suka taru suka naɗa Abimelek sarki kusa da itacen oak na al'amudin da yake a Shekem.
7 Da Yotam ya ji wannan sai ya tafi, ya tsaya a kan Dutsen Gerizim, da babbar murya, ya ce musu, “Ku kasa kunne gare ni ku mutanen Shekem, domin kuma Allah ya kasa kunne gare ku!
8 Wata rana itatuwa suka taru don su naɗa wa kansu sarki. Suka ce wa itacen zaitun, ‘Kai ka zama sarkinmu.’
9 Amma itacen zaitun ya ce musu, ‘In bar maina wanda da shi ake girmama alloli da mutane, don in tafi in yi ta fama da itatuwa?’