53 Amma wata mace ta jefi Abimelek da ɗan dutsen niƙa a kā, ƙoƙon kansa ya ragargaje.
54 Nan da nan sai Abimelek ya kira saurayin da yake ɗaukar masa makamai, ya ce masa, “Ka zaro takobinka, ka kashe ni domin kada mutane su ce, ‘Mace ta kashe shi.’ ” Sai saurayin ya soki Abimelek, ya mutu.
55 Da Isra'ilawa suka ga Abimelek ya mutu, sai dukansu suka tafi gida.
56 Ta haka Allah ya saƙa wa Abimelek muguntar da ya yi wa mahaifinsa, da ya kashe 'yan'uwansa maza, su saba'in.
57 Haka kuwa Allah ya sa muguntar mutanen Shekem ta koma kansu. Bakin Yotam, ɗan Yerubba'al, kuma ya kama su.