13 A duniyar nan na ga wani babban al'amari game da hikima.
14 Dā akwai wani ɗan ƙaramin gari, mutane kuma suke ciki. Sai wani babban sarki ya kawo masa yaƙi, ya kafa masa babban sansani.
15 Akwai wani matalauci, mai hikima, a garin, sai ya ceci garin ta wurin hikimarsa. Duk da haka ba wanda ya tuna da wannan matalauci.
16 Na ce hikima ta fi ƙarfe ƙarfi, ko da yake an raina hikimar matalauci da maganarsa.
17 Gara a kasa kunne ga tattausar maganar mai hikima, da a kasa kunne ga hargagin mai mulki a tsakanin wawaye.
18 Hikima ta fi makaman yaƙi, amma mai zunubi ɗaya yakan yi ɓarna mai yawa.