28 Za ku zama la'anannu idan ba ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku ba, amma kuka kauce daga hanyar da nake umartarku da ita yau, har ku bi waɗansu alloli waɗanda ba ku san su ba.
29 Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya kai ku cikin ƙasar da za ku shiga ku mallake ta, sai ku ɗibiya albarkar a Dutsen Gerizim, ku ɗibiya la'anar kuma a Dutsen Ebal.
30 Duka biyunsu suna hayin Urdun ne, yamma da hanya a ƙasar Kan'aniyawa, mazaunan Araba, kusa da Gilgal, wajen itacen oak na More.
31 Gama za ku haye Urdun, ku shiga ƙasar da za ku mallaka, wadda Ubangiji Allahnku yake ba ku. Sa'ad da kuka mallake ta, kuka zauna a ciki,
32 sai ku lura, ku aikata dukan dokoki da farillai waɗanda nake sawa a gabanku yau.”