M. Sh 2 HAU

Shekarun da suka Yi a Jeji

1 “Muka koma cikin jeji ta hanyar Bahar Maliya kamar yadda Ubangiji ya faɗa mini. Muka daɗe muna ta gewaya ƙasar tuddai ta Seyir.

2 “Sai Ubangiji ya ce mini.

3 ‘Ai, kun daɗe kuna ta gewaya waɗannan tuddai. Ku juya, ku nufi arewa.

4 Ka umarci jama'a, su bi yankin ƙasar zuriyar Isuwa, danginku, waɗanda suke zaune a Seyir. Za su ji tsoronku, sai ku yi hankali,

5 kada ku tsokane su, gama ko wurin sa ƙafa a ƙasarsu ba zan ba ku ba, gama na riga na ba Isuwa ƙasar tuddai ta Seyir.

6 Za ku sayi abincin da za ku ci, da ruwan da za ku sha a wurinsu.

7 Gama Ubangiji Allahnku ya sa albarka a kan dukan ayyukan hannuwanku. Ya kuma san tafiye-tafiyenku cikin babban jejin nan. Ubangiji Allahnku yana tare da ku a shekara arba'in ɗin nan, ba ku rasa kome ba.’

8 “Muka yi gaba, muka bar zuriyar Isuwa 'yan'uwan nan namu waɗanda suke zaune a ƙasar tuddai ta Seyir, muka bar hanyar Araba, da hanyar Elat da Eziyon-geber. Muka juya, muka nufi wajen jejin Mowab.

9 “Sai Ubangiji ya ce mini, ‘Kada ku dami Mowabawa, ko kuwa ku tsokane su, gama ba zan ba ku ƙasarsu ku mallake ta ba. Na riga na bayar da Ar ta zama mallakar zuriyar Lutu.’ ”

10 (Emawa manya ne, masu yawa, dogaye ne kuma kamar Anakawa. Su ne suke zaune a ƙasar a dā.

11 Su ma akan lasafta su Refayawa tare da Anakawa, amma Mowabawa suka ce da su Emawa.

12 Haka nan kuma a dā Horiyawa ne suke zaune a ƙasar Seyir, amma mutanen zuriyar Isuwa suka zo, suka kore su, suka karkashe su, suka zauna a wurin, daidai kamar yadda Isra'ilawa suka yi da ƙasar mallakarsu, wadda Ubangiji ya ba su.)

13 “ ‘Yanzu, ku tashi ku haye rafin Zered da kanku.’ Sai kuwa muka haye.

14 Lokacin da muka tashi daga Kadesh-barneya zuwa lokacin da muka haye rafin Zered, shekara talatin da takwas ne. Duk wannan lokaci dukan waɗanda suka isa yaƙi suka murmutu kamar yadda Ubangiji ya rantse a kansu.

15 Hakika kuwa ikon Ubangiji ya buge su har suka hallaka ƙaƙaf.

16 “Sa'ad da dukan waɗanda suka isa yaƙi suka mutu,

17 sai Ubangiji ya yi mini magana, ya ce,

18 ‘Yau za ku ratsa kan iyakar ƙasar Mowab a Ar.

19 Sa'ad da ku kuka zo kusa da Ammonawa, kada ku dame su, ko ku tsokane su, gama ba zan ba ku abin mallaka daga yankin ƙasar Ammonawa ba, domin na ba da ita ta zama mallaka ga zuriya Lutu.’ ”

20 (Ita ma aka lasafta ta ƙasar Refayawa ce. Dā Refayawa waɗanda Ammonawa suke kira Zuzawa, su ne suka zauna cikinta.

21 Manyan mutane masu yawa dogaye ne kuma kamar Anakawa, amma Ubangiji ya hallakar da su a gabansu, suka kore su, suka zauna a wurinsu,

22 daidai kamar yadda Ubangiji ya yi wa zuriyar Isuwa waɗanda suka zauna a Seyir, sa'ad da ya hallakar da Horiyawa a gabansu. Su kuma suka kore su suka zauna a wurinsu har wa yau.

23 Haka nan kuma ya faru da Awwiyawa mazaunan ƙauyukan da suke kewaye da Gaza, wato su Kaftorawa waɗanda suka zo daga Kaftor, suka hallakar da su, suka zauna a wurinsu.)

24 “Ubangiji ya ce, ‘Ku tashi, ku kama hanya, ku haye kwarin Arnon. Duba, na ba da Sihon Ba'amore, Sarkin Heshbon, da ƙasarsa a hannunku, ku fara mallakar ƙasar, ku yaƙe shi.

25 A wannan rana ce zan fara sa al'ummai ko'ina a duniya su razana, su ji tsoronku. Sa'ad da za su ji labarinku, za su yi rawar jiki, su damu ƙwarai.’ ”

Isra'ilawa Sun Ci Sihon

26 “Sa'an nan na aiki manzanni daga jejin Kedemot zuwa Sihon, Sarkin Heshbon, ina neman zaman lafiya, na ce,

27 ‘Ka yardar mini in bi ta cikin ƙasarka. Zan bi ta kan babbar hanya sosai, ba zan ratse dama ko hagu ba.

28 Zan sayi abincin da zan ci, da ruwan da zan sha a wurinku.

29 Kai dai ka yardar mini in bi in wuce kamar yadda zuriyar Isuwa, mazaunan Seyir, da Mowabawa, mazaunan Ar, suka yardar mini. Gama ina so in haye Urdun zuwa ƙasa wadda Ubangiji Allahnmu yake ba mu.’

30 “Amma Sihon, Sarkin Heshbon, ya ƙi yarda mu wuce, gama Ubangiji Allahnku ya riga ya taurare hankalinsa da zuciyarsa don ya bashe shi a hannunku, kamar yadda yake a yau.

31 “Sai Ubangiji ya ce mini, ‘Duba, na fara ba da Sihon da ƙasarsa a gare ku. Ku fara fāɗa wa ƙasarsa da yaƙi don ku mallake ta.’

32 Sai Sihon da mutanensa suka fita su gabza yaƙi da mu a Yahaza.

33 Ubangiji Allahnmu ya bashe shi a hannunmu, muka ci nasara a kansa, da 'ya'yansa, da dukan mutanensa.

34 Muka ci dukan garuruwansa, muka hallaka kowane gari, da mata, da maza, da yara, ko ɗaya bai ragu ba.

35 Sai dabbobi ne kaɗai da dukiyar garuruwan da muka ci, su ne muka kwashe ganima.

36 Daga Arower wadda take gefen kwarin kogin Arnon, zuwa Gileyad har ma da garin da yake cikin kwarin, Ubangiji Allahnmu ya ba da dukan kome a gare mu. Ba birnin da ya gagare mu.

37 Amma ba ku kusaci ƙasar Ammonawa ba, wato ƙasar da take a kwarin kogin Yabbok, da garuruwan ƙasar tuddai, da wuraren da Ubangiji Allahnmu ya hana mu.”

Surori

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34