1 “Idan wani annabi, ko mai mafarki ya fito a cikinku, ya yi muku shelar wata alama ko mu'ujiza,
2 idan alamar ko mu'ujizar ta auku, idan kuma ya ce, ‘Bari mu bi gumaka, mu bauta musu, gumakan da ba ku san su ba,
3 kada ku saurari maganar annabin nan ko mai mafarkin nan, gama Ubangiji Allahnku yana jarraba ku ne, ya gani, ko kuna ƙaunarsa da zuciya ɗaya da dukan ranku.
4 Sai ku bi Ubangiji Allahnku, ku yi tsoronsa, ku kiyaye umarnansa, ku kasa kunne ga muryarsa, shi ne za ku bauta masa, ku manne masa kuma.