14 da kowane irin hankaka,
15 da jimina, da ƙururu, da bubuƙuwa, da kowane irin shaho,
16 da mujiya, da babbar mujiya, da ɗuskwi,
17 da kwasakwasa, da ungulu, da dimilmilo,
18 da zalɓe, da kowane irin jinjimi, da katutu, da yaburbura.
19 “Dukan 'yan ƙwari masu fikafikai masu rarrafe haram ne a gare ku, kada ku ci su.
20 Za ku iya cin duk abin da yake da fikafikai in dai shi halattacce ne.