1 “Kada ku miƙa wa Ubangiji Allahnku hadaya da sa ko da tunkiyar da take da lahani ko naƙasa, gama wannan abar ƙyama ce ga Ubangiji Allahnku.
2 “Idan aka sami wata, ko wani, daga cikin wani gari da Ubangiji Allahnku yake ba ku, yana aikata abin da yake mugu a gaban Ubangiji Allahnku, yana karya alkawarinsa,
3 har ya je, ya bauta wa gumaka, ya yi musu sujada, ko rana, ko wata, ko ɗaya daga cikin rundunar sama, ya yi abin da na hana,
4 idan aka faɗa muku, ko kuwa kun ji labarinsa sai ku yi cikakken bincike. Idan gaskiya ce, aka kuma tabbata an yi wannan mugun abu cikin Isra'ilawa,
5 to, ku kawo macen, ko mutumin, da ya aikata wannan mugun abu a bayan ƙofar garinku, nan za ku jajjefe shi da duwatsu har ya mutu.
6 Bisa ga shaidar mutum biyu ko uku za a kashe shi, amma ba za a kashe mutum a kan shaidar mutum ɗaya ba.
7 Sai shaidun su fara jifansa sa'an nan sauran jama'a su jajjefe shi. Ta haka za a kawar da mugunta daga cikinsu.