2 Ba za su sami gādo tare da 'yan'uwansu ba, Ubangiji ne gādonsu kamar yadda ya alkawarta musu.
3 “To, ga rabon da jama'a za su ba firistoci daga hadayun da suka miƙa, ko sā ne ko tunkiya ce, sai su ba firistoci kafaɗar, da kumatun, da tumbin.
4 Sai kuma ku ba su nunan fari na hatsinku, da ruwan inabinku, da manku, da kuma gashin tumakinku wanda kuka fara sausaya.
5 Gama Ubangiji Allahnku ya zaɓe su, su da 'ya'yansu, daga dukan kabilanku don su yi aiki da sunan Ubangiji har abada.
6 “Balawe yana da dama ya tashi daga kowane gari na Isra'ila inda yake zaune ya je wurin da Ubangiji ya zaɓa.
7 Idan ya zo, sai ya yi aiki saboda sunan Ubangiji Allahnku kamar sauran 'yan'uwansa Lawiyawa waɗanda suke aiki a gaban Ubangiji a can.
8 Zai sami rabon abincinsa daidai da saura, har da abin da yake na kakanninsa wanda ya sayar.”