1 “Idan kun ga ɓataccen san wani, ko tunkiyarsa, to, kada ku ƙyale shi, amma lalle sai ku komar da shi ga mai shi.
2 Idan mutumin ba kusa da ku yake zaune ba, ko kuma ba ku san shi ba, to, sai ku kawo dabbar a gidanku, ta zauna a wurinku, har lokacin da mutumin ya zo ya shaida ta, sa'an nan ku ba shi.
3 Haka nan kuma za ku yi da jakinsa, da riga, da kowane abin wani da ya ɓace, ku kuwa kuka tsinta. Faufau, kada ku ƙyale su.
4 “Idan kun ga jakin wani ko sansa ya faɗi a hanya, kada ku ƙyale shi, sai ku taimake shi ku tashe shi.