22 Idan kun nisanci yin wa'adi, ba zai zama zunubi gare ku ba.
23 Sai ku cika duk abin da kuka faɗa da bakinku, gama da yardarku ne kuka yi wa Ubangiji Allahnku wa'adi wanda kuka alkawarta.
24 “Sa'ad da kuka shiga gonar inabin maƙwabcinku, kuna iya cin 'ya'yan inabin, har ku ƙoshi yadda kuke so, amma kada ku sa wani a jakarku.
25 Sa'ad da kuka shiga hatsin maƙwabcinku da yake tsaye, kun iya ku yi murmuren tsabar da hannunku, amma kada ku sa wa hatsin maƙwabcinku lauje.”