5 “Idan mutum ya yi sabon aure, kada ya tafi yaƙi tare da sojoji, ko kuma a sa shi kowane irin aiki. Sai ya huta a gida har shekara ɗaya saboda gidansa, don ya faranta wa matar da ya auro zuciya.”
6 “Kada mutum ya karɓi jinginar dutsen niƙa ko ɗan dutsen niƙa, gama yin haka karɓar jinginar rai ne.
7 “Idan aka iske mutum yana satar danginsa Ba'isra'ile don ya maishe shi bawansa, ko ya sayar da shi, sai a kashe ɓarawon. Ta haka za ku kawar da mugunta daga tsakiyarku.
8 “Game da ciwon kuturta, sai ku lura ku bi daidai da yadda firistoci na Lawiyawa suka umarce ku, ku yi. Sai ku kiyaye, ku aikata yadda na umarce su.
9 Ku tuna da abin da Ubangiji Allahnku ya yi wa Maryamu a lokacin da kuka fito daga Masar.
10 “Idan kun ba maƙwabcinku rance na kowane iri, kada ku shiga gidansa don ku ɗauki jingina.
11 Sai ku tsaya a waje, mutumin da kuka ba shi rancen zai kawo muku jinginar.