5 “Idan 'yan'uwa suna zaune wuri ɗaya tare, in ɗayansu ya rasu bai haihu ba, to, kada matar marigayin ta auri wani baƙo wanda yake ba a cikin dangin mijin ba. Sai ɗan'uwan mijinta ya zo wurinta, ya aure ta, ya yi mata abin da ya kamaci ɗan'uwan miji ya yi.
6 Ɗan farin da za ta haifa, zai zama magajin marigayin don kada a manta da sunansa cikin Isra'ila.
7 Amma idan mutum ya ƙi ya auri matar ɗan'uwansa, marigayi, sai matar ta tafi wurin dattawa a dandalin ƙofar gari, ta ce, ‘Ɗan'uwan mijina, marigayi, ya ƙi wanzar da sunan ɗan'uwansa cikin Isra'ila, gama ya ƙi yi mini abin da ya kamaci ɗan'uwan marigayi, ya yi.’
8 Sai dattawan garin su kira mutumin, su yi masa magana. Idan ya nace, yana cewa, ‘Ba na so in aure ta,’
9 sai matar ɗan'uwansa, marigayi, ta tafi wurinsa a gaban dattawan, ta kwaɓe takalmin ƙafarsa, ta tofa masa yau a fuskarsa, ta ce, ‘Haka za a yi wa wanda ya ƙi kafa gidan ɗan'uwansa.’
10 Za a kira sunan gidansa cikin Isra'ila, ‘Gidan wanda aka kwaɓe masa takalmi.’ ”
11 “Idan mutane biyu suna faɗa da juna, idan matar mutum ɗaya daga cikinsu ta zo don ta taimaki mijinta, idan ta kama marainan wancan mutum da hannunta,