1 “Sa'ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku gāda, kuka mallake ta, kuka zauna cikinta,
2 to, sai ku keɓe nunan fari na dukan amfanin ƙasa wanda kuka shuka a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku. Ku sa cikin kwando, ku tafi inda Ubangiji Allahnku zai zaɓa don ya tabbatar da sunansa.
3 Ku je wurin firist wanda yake aiki a lokacin, ku ce, ‘Yau, na sakankance a gaban Ubangiji Allahnka, cewa na shiga ƙasar da Ubangiji ya rantse wa kakanninmu zai ba mu.’
4 “Sa'an nan firist ya karɓi kwandon daga gare ku ya sa shi kusa da bagaden Ubangiji Allahnku.