3 Ku je wurin firist wanda yake aiki a lokacin, ku ce, ‘Yau, na sakankance a gaban Ubangiji Allahnka, cewa na shiga ƙasar da Ubangiji ya rantse wa kakanninmu zai ba mu.’
4 “Sa'an nan firist ya karɓi kwandon daga gare ku ya sa shi kusa da bagaden Ubangiji Allahnku.
5 Sa'an nan kuma sai ku hurta waɗannan kalmomi a gaban Ubangiji Allahnku, ku ce, ‘Ubana Ba'aramiye ne, mayawaci a dā. Ya gangara zuwa Masar yana da jama'a kima, ya yi baƙunci a wurin. Amma a can ya zama al'umma mai girma, mai iko, mai yawa.
6 Masarawa suka wulakanta mu, suka tsananta mana, suka bautar da mu.
7 Amma muka yi kuka ga Ubangiji Allah na kakanninmu. Ubangiji kuwa ya ji kukanmu, ya ga azabarmu, da wahalarmu, da zaluncin da ake yi mana.
8 Sai Ubangiji ya fisshe mu daga Masar da dantsensa mai ƙarfi, mai iko, tare da bantsoro, da alamu, da mu'ujizai.
9 Ubangiji ya kawo mu nan, ya ba mu ƙasar nan, ƙasar da take mai yalwar abinci.