20 “ ‘La'ananne ne wanda ya kwana da matar mahaifinsa, gama ya buɗe fatarin matar mahaifinsa.’“Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’
21 “ ‘La'ananne ne wanda ya kwana da dabba.’“Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’
22 “ ‘La'ananne ne wanda ya kwana da 'yar'uwarsa, wato 'yar mahaifinsa, ko 'yar mahaifiyarsa.’“Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’
23 “ ‘La'ananne ne wanda ya kwana da surukarsa.’“Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’
24 “ ‘La'ananne ne wanda ya buge maƙwabcinsa daga ɓoye.’“Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!”
25 “ ‘La'ananne ne wanda aka yi ijara da shi don ya kashe marar laifi.’“Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’
26 “ ‘La'ananne ne wanda bai yi na'am da kalmomin dokokin nan don ya yi aiki da su ba.’“Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’ ”