23 “ ‘La'ananne ne wanda ya kwana da surukarsa.’“Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’
24 “ ‘La'ananne ne wanda ya buge maƙwabcinsa daga ɓoye.’“Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!”
25 “ ‘La'ananne ne wanda aka yi ijara da shi don ya kashe marar laifi.’“Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’
26 “ ‘La'ananne ne wanda bai yi na'am da kalmomin dokokin nan don ya yi aiki da su ba.’“Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’ ”