1 “Idan kun yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, kuna aikata dukan umarnansa waɗanda nake umartarku da su yau, to, Ubangiji Allahnku zai fifita ku fiye da dukan sauran al'umma.
2 Idan kun yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, dukan albarkun nan za su sauko muku, su zama naku.
3 “Za ku zama masu albarka, ko kuna cikin gari, ko kuna cikin karkara.
4 “'Ya'yanku za su zama masu albarka, haka nan kuma amfanin gonakinku, da 'ya'yan dabbobinku, da 'ya'yan shanunku, da 'ya'yan tumakinku da awakinku.
5 “Kwandunanku da makwaɓan za su yalwata ƙullunku.