26 Suka tafi suka bauta wa gumaka, suka yi musu sujada, gumakan da ba su san su ba, ba Ubangiji ne ya ba su ba.
27 Saboda haka Ubangiji ya husata da wannan ƙasa, ya kawo mata kowace irin la'anar da aka rubuta a wannan littafin.
28 Ubangiji ya tumɓuke su da zafin fushinsa, da babbar hasala, daga ƙasarsu, ya watsa su cikin wata ƙasa dabam kamar yadda suke a yau.’
29 “Sanin gaibu na Ubangiji Allahnmu ne, amma abubuwan da aka bayyana namu ne, mu da 'ya'yanmu har abada, don mu kiyaye dukan maganar dokokin nan.”