19 Ku lura fa, sa'ad da kuka dubi sama, kuka ga rana, da wata, da taurari, da dai dukan rundunar sama, don kada fa ku jarabtu, ku yi musu sujada, ko ku bauta musu. Ubangiji Allahnku ya sa waɗannan saboda dukan al'ummai.
20 Amma ku, Ubangiji ya fisshe ku daga gidan bauta mai zafi, wato Masar, don ku zama jama'arsa ta musamman kamar yadda kuke a yau.
21 Amma Ubangiji ya yi fushi da ni sabili da ku, har ya rantse, cewa ba zan haye Urdun in shiga kyakkyawar ƙasan nan wadda yake ba ku abar gādo ba.
22 Gama a nan ƙasar zan mutu, ba zan haye Urdun ba, amma ku za ku haye, ku mallaki wannan kyakkyawar ƙasa.
23 Saboda haka, ku lura fa, kada ku manta da alkawarin da Ubangiji Allahnku ya yi da ku, don haka kada ku sassaƙa wa kanku wata siffar kowane irin kamanni wanda Ubangiji Allahnku ya hana ku.
24 Gama Ubangiji Allahnku wuta ne mai cinyewa, shi kuma mai kishi ne.
25 “Sa'ad da kuka haifi 'ya'ya, kuka sami jikoki, kuka kuma daɗe cikin ƙasar, idan kuka yi abin da yake haram, wato kuka yi gunki na sassaƙa na kowace irin siffa, kuka kuma aikata mugunta a gaban Ubangiji Allahnku har kuka tsokane shi ya yi fushi,