6 Waɗannan kalmomi da na umarce ku da su a yau, za su zauna a zuciyarku.
7 Sai ku koya wa 'ya'yanku su da himma. Za ku haddace su sa'ad da kuke zaune a gida, da sa'ad da kuke tafiya, da sa'ad da kuke kwance, da sa'ad da kuka tashi.
8 Za ku ɗaura su a hannunku da goshinku don alama.
9 Za ku kuma rubuta su a madogaran ƙofofin gidajenku, da ƙofofinku.”
10 “Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya kai ku ƙasar da ya rantse wa kakanninku Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, zai ba ku manyan birane masu kyau waɗanda ba ku ne kuka gina ba,
11 da gidaje cike da abubuwa masu kyau waɗanda ba ku ne kuka cika su ba, da rijiyoyi waɗanda ba ku ne kuka haƙa ba, da gonakin inabi da itatuwan zaitun waɗanda ba ku ne kuka dasa ba. Sa'ad da kuka ci, kuka ƙoshi,
12 to, kada ku manta da Ubangiji wanda ya fito da ku daga ƙasar Masar, daga gidan bauta.