1 Ubangiji ya duhunta Sihiyona saboda fushinsa!Daga Sama kuma ya jefar da darajar Isra'ila a ƙasa.Bai kuma tuna da matashin sawayensa baA ranar fushinsa.
2 Dukan wuraren zaman Yakubu,Ubangiji ya hallakar ba tausayi,Da fushinsa kuma ya rurrushe kagaran Sihiyona.Ya ƙasƙantar da mulki da masu mulkin.
3 Da zafin fushinsa, ya karya ƙarfin Isra'ila,Ya kuma bar yi musu taimakoA lokacin da abokan gāba suka zo.Kamar harshen wuta, ya ƙone dukan abin da yake na Yakubu.
4 Ya ja bakansa kamar abokan gāba,Ya kuma nuna ikonsa kamar maƙiyi.Ya hallaka dukan abin da yake da bansha'awa.A alfarwar Sihiyona, ya zubo da hasalarsa kamar wuta.