4 Harshen jinjiri ya liƙe a dasashinsa saboda ƙishi,'Yan yara suna roƙon abinci,Amma ba wanda ya ba su.
5 Su waɗanda suka ci abubuwa masu daɗi,Sun halaka a titi.Su waɗanda aka goye su da alharini,Yanzu suna kwance a kan tsibin toka.
6 Gama zunubin mutanenaYa fi zunubin Saduma,Wadda Ubangiji ya hallakar da ita nan da nan.
7 Keɓaɓɓunta sun fi dusar ƙanƙara tsabta,Sun kuma fi madara fari.Jikunansu sun fi murjani ja.Kyan tsarinsu yana kama da shuɗin yakutu.
8 Yanzu fuskokinsu sun fi kukunniya baƙi,Ba a iya fisshe su a titi ba,Fatar jikinsu ta liƙe wa ƙasusuwansu,Sun bushe kamar itace.
9 Gara ma waɗanda takobi ya kasheDa waɗanda yunwa ta kashe,Gama sun rame sarai saboda rashin abinci.
10 Mata masu juyayi, da hannuwansuSuka ɗauki 'ya'yansu, suka dafa,Suka zama musu abinci a lokacin halakar mutanena.