6 Gama zunubin mutanenaYa fi zunubin Saduma,Wadda Ubangiji ya hallakar da ita nan da nan.
7 Keɓaɓɓunta sun fi dusar ƙanƙara tsabta,Sun kuma fi madara fari.Jikunansu sun fi murjani ja.Kyan tsarinsu yana kama da shuɗin yakutu.
8 Yanzu fuskokinsu sun fi kukunniya baƙi,Ba a iya fisshe su a titi ba,Fatar jikinsu ta liƙe wa ƙasusuwansu,Sun bushe kamar itace.
9 Gara ma waɗanda takobi ya kasheDa waɗanda yunwa ta kashe,Gama sun rame sarai saboda rashin abinci.
10 Mata masu juyayi, da hannuwansuSuka ɗauki 'ya'yansu, suka dafa,Suka zama musu abinci a lokacin halakar mutanena.
11 Ubangiji ya saki fushinsa,Ya zuba fushinsa mai zafi.Ya kunna wa Sihiyona wutaWadda ta cinye harsashin gininta.
12 Sarakunan duniya da mazaunanta ba su gaskata,Cewa abokan gaba ko maƙiyaZa su iya shiga ƙofofin Urushalima ba.