4 Duwatsu za su narke aƙarƙashinsa,Kwaruruka za su tsattsage kamarkakin zuma a gaban wuta,Kamar ruwa yana gangarowa dagatsauni.
5 Duk wannan kuwa saboda laifinYakubu ne,Da laifin Isra'ila.Mene ne laifin Yakubu?Ashe, ba bautar gumaka da zaluncinda ake yi a Samariya ba?Mene ne kuma laifin Yahuza?Ashe, ba bautar gumaka da zaluncinda ake yi a Urushalima ba?
6 “Domin haka zan mai da Samariyajujin kufai a karkara,Wurin dasa kurangar inabi.Zan zubar da duwatsunta a cikinkwari,In tone harsashin gininta.
7 Za a farfashe dukan siffofinta nazubi,Za a ƙaƙƙone dukiyarta da wuta,Zan lalatar da gumakanta duka,Gama ta wurin karuwanci ta samosu,Ga karuwanci kuma za su koma.”
8 Mika ya ce, “Saboda wannan zan yibaƙin ciki, in yi kuka,Zan tuɓe, in yi tafiya huntu.Zan yi kuka kamar diloli,In yi baƙin ciki kamar jiminai.
9 Gama raunin Samariya, ba yawarkuwa,Gama ya kai Yahuza,Ya kuma kai ƙofar jama'ata aUrushalima.”
10 Kada a faɗe shi a Gat,Sam, kada a yi kuka.Yi birgima cikin ƙura a Bet-leyafra.