4 A wannan rana za su yi karinmagana a kanku,Za su yi kuka da baƙin ciki maizafi,Su ce, “An lalatar da mu sarai!Ya sāke rabon mutanena,Ya kawar da shi daga gare ni!Ya ba da gonakinmu ga waɗandasuka ci mu da yaƙi.”
5 Don haka ba za ku sami wanda zai samuku ma'auniA taron jama'ar Ubangiji ba.
6 “Kada su yi wa'azi,” amma sun yiwa'azi.“Idan ba su yi wa'azi a kanabubuwan nan ba,Raini ba zai ƙare ba.
7 Daidai ne a faɗi haka, ya jama'arYakubu?‘Ruhun Ubangiji ya yi rashin haƙurine?Waɗannan ayyukansa ne?’ ”“Ashe, maganata ba takan amfanawanda yake tafiya daidai ba?”
8 Ubangiji ya amsa ya ce,“Ba da daɗewa ba mutanena suntashi kamar maƙiyi,Kukan tuɓe rigar masu wucewa dasalama, masu komawa da yaƙi.
9 Kukan kori matan mutanenaDaga gidajensu masu kyau,Kukan kawar da darajata har abadadaga wurin 'ya'yansu.
10 Ku tashi, ku tafi,Gama nan ba wurin hutawa ba ne,Saboda ƙazantarku wadda take kawomuguwar hallaka.