1 Ki tattara sojojinki, gama ankewaye mu da yaƙi.Za su bugi kumatun Sarkin Isra'ilada sanda.”
2 “Baitalami cikin Efrata,Wadda kike 'yar ƙarama a cikinkabilar Yahuza,Amma daga cikinki wani zai fitowanda zai sarauci Isra'ilaWanda asalinsa tun fil azal ne.”
3 Domin haka zai yashe su,Sai lokacin da wadda take naƙuda tahaihu.Sa'an nan sauran 'yan'uwansaZa su komo wurin mutanen Isra'ila.
4 Shi kuwa zai tashi ya ciyar dagarkensa da ƙarfin Ubangiji,Da ɗaukakar sunan UbangijiAllahnsa.Za su kuwa zauna lafiya,Gama zai zama mai girma cikinduniya duka.