2 “Baitalami cikin Efrata,Wadda kike 'yar ƙarama a cikinkabilar Yahuza,Amma daga cikinki wani zai fitowanda zai sarauci Isra'ilaWanda asalinsa tun fil azal ne.”
3 Domin haka zai yashe su,Sai lokacin da wadda take naƙuda tahaihu.Sa'an nan sauran 'yan'uwansaZa su komo wurin mutanen Isra'ila.
4 Shi kuwa zai tashi ya ciyar dagarkensa da ƙarfin Ubangiji,Da ɗaukakar sunan UbangijiAllahnsa.Za su kuwa zauna lafiya,Gama zai zama mai girma cikinduniya duka.
5 Zai zama salamarmu.Sa'ad da kuma Assuriyawa za sukawo mana yaƙi,Za su tattake kagaranmu,Za mu sa makiyaya bakwai dashugabanni takwas su yi gāba dasu.
6 Za su mallaki ƙasar Assuriya datakobi,Su shiga ƙofofin ƙasar Nimrod dazararren takobi,Zai cece mu daga hannunBa'assuriye,Sa'ad da ya kawo wa ƙasarmuyaƙi,Sa'ad da kuma ya tattake ƙasarmu.
7 Sa'an nan ringin Yakubu zai zamarwa mutaneKamar raɓa daga wurin Ubangiji,Kamar kuma yayyafi a kan tsire-tsire,Wanda ba ya jinkiri ko ya jiramutane.
8 Ringin Yakubu kuma zai zamar waal'umman duniya,Kamar yadda zaki yake a tsakaninnamomin jeji,Kamar kuma yadda zaki yake atsakanin garkunan tumaki,Wanda, sa'ad da ya ratsa, yakantattaka,Ya yi kacakaca da su,Ba wanda zai cece su.