1 “Ku ji abin da ni Ubangijinake cewa,Tashi ku gabatar da ƙararku agaban duwatsu,Ku bar tuddai su ji muryarku.
2 “Ku duwatsu da madawwaman tussanduniya,Ku ji tuhumar da Ubangiji yake yimuku.Gama Ubangiji, yana da maganagāba da mutanensa,Zai tuhumi Isra'ila.
3 “Ya ku jama'ata, me na yi muku?Wace irin fitina nake yi muku?Ku amsa mini!
4 Gama na fito da ku daga ƙasarMasar,Na fanshe ku daga gidan bauta.Na aika muku da Musa, da Haruna,da Maryamu.