4 Gama na fito da ku daga ƙasarMasar,Na fanshe ku daga gidan bauta.Na aika muku da Musa, da Haruna,da Maryamu.
5 Ya ku jama'ata, ku tunaDa abin da Balak, Sarkin Mowab, yaƙulla,Da yadda Bal'amu ɗan Beyor yaamsa masa,Da abin da ya faru daga Shittim, harzuwa Gilgal,Don ku san ayyukan adalci naUbangiji.”
6 Da me zan zo gaban Ubangiji,In sunkuyar da kaina a gaban Allahna Sama?Ko in zo gabansa da maraƙi banaɗaya domin yin hadaya taƙonawa?
7 Ubangiji zai yi murna da ragunadubbaiKo kuwa da kogunan mai dubbai?Zan ba da ɗan farina ne donlaifina?Ko kuwa zan ba da 'ya'yana sabodazunubina?
8 Ya kai mutum, ya riga ya nunamaka abin da yake mai kyau.Abin da Ubangiji yake so gare ka,shi neKa yi adalci, ka ƙaunaci aikataalheri,Ka bi Allah da tawali'u.
9 Ubangiji yana kira ga birnin.Hikima ce ƙwarai a ji tsoronsunanka.“Ki ji ya kabila, wa ya sa mikilokacinki?
10 Ba zan manta da dukiya ta muguntaa gidan mugu ba,Ba kuwa zan manta da bugaggenmudun awo ba.