7 Dukan waɗanda za su dube kiZa su ja da baya su ce,‘Nineba ta lalace, wa zai yi kukadominta?’A ina zan samo miki waɗanda za suta'azantar da ke?”
8 Kin fi No ne?Wadda take a bakin Nilu,Wadda ruwa ya kewaye ta?Teku ce kagararta.Ruwa ne kuma garunta.
9 Habasha da Masar su ne ƙarfintamarar iyaka,Fut da Libiya su ne kumamataimakanta.
10 Duk da haka an tafi da ita, an kai tacikin bauta.An fyaɗa ƙanananta a ƙasa,An yi kacakaca da su a kowacemararraba.An jefa kuri'a a kan manyanmutanenta,Aka ɗaure dukan manyan mutanentada sarƙoƙi.
11 Ke Nineba kuma za ki bugu,Za a ɓoye ki.Za ki nemi mafaka a wurin maƙiyinki.
12 Dukan kagaranki suna kama daitatuwan ɓaure,Waɗanda 'ya'yansu suka harba.Da an girgiza sai su faɗo a bakin maisha.
13 Sojojinki kamar mata suke atsakiyarki!An buɗe wa maƙiyanki ƙofofinƙasarki.Wuta za ta cinye madogaranƙofofinki.