Neh 10:2-8-31 HAU

2-8 sa'an nan firistoci, watoSeraiya, da Azariya, da Irmiya,Fashur, da Amariya, da Malkiya,Hattush, da Shebaniya, da Malluki,Harim, da Meremot, da Obadiya,Daniyel, da Ginneton, da Baruk,Meshullam, da Abaija, da Miyamin,Mawaziya, da Bilgai, da Shemaiya.

9-13 Wajen Lawiyawa kuwa, su neYeshuwa ɗan Azaniya, da Binnuyi daga zuriyar Henadad da Kadmiyel.'Yan'uwansu kuwa su ne Shebaniya, da Hodiya,Kelita, da Felaya, da Hanan,Mika, da Rehob, da Hashabiya,Zakkur, da Sherebiya, da Shebaniya,Hodiya, da Bani, da Beninu.

14-27 Shugabannin jama'a kuwa, su ne Farosh, da Fahat-mowab,Elam, da Zattu, da Bani,Bunni, da Azgad, da Bebai,Adonaija, da Bigwai, da Adin,Ater, da Hezekiya, da Azzur,Hodiya, da Hashum, da Bezai,Harif, da Anatot, da Nebai,Magfiyash, da Meshullam, da Hezir,Meshezabel, da Zadok, da Yadduwa,Felatiya, da Hanan, da Anaya,Hosheya, da Hananiya, da Hasshub,Hallohesh, da Filha, da Shobek,Rehum, da Hashabna, da Ma'aseya,Ahaija, da Hanan, da Anan,Malluki, da Harim, da Ba'ana.

28 Jama'ar Isra'ila, da firistoci, da Lawiyawa, da masu tsaron ƙofofi, da mawaƙa, da ma'aikatan Haikali, da dukan waɗanda suka ware kansu daga sauran al'umman waɗansu ƙasashe, domin su bi dokokin Allah, su da matansu, da 'ya'yansu mata da maza, da dai duk waɗanda suke da sani da fahimta,

29 suka haɗa kai da 'yan'uwansu, da shugabanninsu, suka rantse, cewa la'ana ta same su idan ba su kiyaye dokokin Allah waɗanda ya ba bawansa Musa ba. Suka rantse za su kiyaye, su aikata umarnai, da ka'idodi, da dokokin Ubangijinmu.

30 Suka ce, “Ba za mu aurar wa mutanen ƙasar da 'ya'yanmu mata ba. Ba kuma za mu auro wa 'ya'yanmu maza 'ya'yansu mata ba.

31 “Idan kuma mutanen ƙasar sun kawo kayayyaki da hatsi don sayarwa a ranar Asabar, ba za mu saya ba, ko kuma a wata tsattsarkar rana.“A kowace shekara ta bakwai ba za mu girbe amfanin gonakinmu ba, za mu kuma yafe kowane irin bashi.