Neh 13 HAU

Gyare-gyaren da Nehemiya Ya Yi

1 A wannan rana aka karanta daga littafin Musa a kunnuwan jama'a. A cikinsa aka tarar da inda aka rubuta, cewa kada Ba'ammone, ko mutumin Mowab ya shiga taron jama'ar Allah.

2 Gama ba su taryi jama'ar Isra'ila da abinci da abin sha ba, amma suka yi ijara da Bal'amu ya zo ya la'anta musu su, amma Allahnmu ya juyar da la'anar ta zama albarka.

3 Da mutane suka ji dokokin, sai suka ware dukan waɗanda suke ba Isra'ilawa ba.

4 Kafin wannan lokaci Eliyashib, firist, wanda aka sa shi shugaban ɗakunan ajiya na Haikalin Allahnmu, wanda yake da dangantaka da Tobiya,

5 ya shirya wa Tobiya babban ɗaki inda dā aka ajiye hadaya ta gari, da turare, da tasoshi, da zakar hatsi, da ruwan inabi, da mai, waɗanda aka umarta a ba Lawiyawa, da mawaƙa, da masu tsaron ƙofofi, da inda aka ajiye sadakokin da ake ba firistoci.

6 Ba na nan a Urushalima sa'ad da wannan abu ya faru, gama a shekara ta talatin da biyu ta sarautar Artashate, Sarkin Babila, na tafi wurin sarki. Daga baya sarki ya ba ni izini in koma.

7 Da na komo Urushalima, sai na ga mugun abin da Eliyashib ya yi domin Tobiya, yadda ya shirya masa ɗaki a filin Haikalin Allah.

8 Sai na husata ƙwarai, na fitar da kayan ɗakin Tobiya a waje.

9 Sai na umarta, suka kuwa tsarkake ɗakunan, sa'an nan na mayar da tasoshin Haikalin Allah, da hadaya ta gari, turare a ciki.

10 Na kuma iske ba a ba Lawiyawa rabonsu ba. Saboda wannan Lawiyawa da mawaƙa masu hidima suka watse zuwa gonakinsu.

11 Sai na yi wa shugabanni faɗa, na ce, “Me ya sa aka ƙi kula da Haikalin Allah?” Sa'an nan na tara Lawiyawa da mawaƙa, na sa su a wuraren aikinsu.

12 Sai dukan mutanen Yahuza suka kawo zakar hatsi, da ta ruwan inabi, da ta mai, a ɗakunan ajiya.

13 Sai na sa Shelemiya, firist, da Zadok, magatakarda, da Fedaiya daga cikin Lawiyawa su zama masu lura da ɗakunan ajiya. Na kuma sa Hanan ɗan Zakkur, jikan Mattaniya ya yi aiki tare da su, gama su amintattu ne. Aikinsu shi ne su raba wa 'yan'uwansu abin da aka kawo.

14 “Ka tuna da ni, ya Allahna, saboda wannan. Kada ka manta da ayyukan kirki da na yi a Haikalin Allah da kuma na hidimarsa.”

15 A kwanakin nan na ga mutane a Yahuza suna matse ruwan inabi, suna labta wa jakunansu buhunan hatsi, da ruwan inabi, da 'ya'yan inabi, da ɓaure, da kaya iri iri, suna kawo su cikin Urushalima a ran Asabar. Sai na yi musu faɗa a kan sayar da abinci a wannan rana.

16 Mutanen Taya da suke zaune a birnin sukan kawo kifi da kaya iri iri, su sayar wa mutanen Yahuza a Urushalima a ranar Asabar.

17 Sai na tsauta wa manyan mutanen Yahuza, na ce musu, “Wane irin mugun abu ne kuke yi haka, kuna ɓata ranar Asabar?

18 Ashe, ba haka kakanninku suka yi ba, har wannan ya sa Allahnmu ya kawo mana masifa, mu da dukan birnin? Duk da haka kuna ƙara kawo wa Isra'ila hasala saboda kuna ɓata ranar Asabar.”

19 Magariba na yi kafin ranar Asabar, sai na yi umarni a rufe ƙofofin Urushalima, kada a buɗe su sai Asabar ta wuce. Na sa waɗansu barorina a ƙofofin, don kada su bari a shigo da kaya ran Asabar.

20 Sau ɗaya ko sau biyu, 'yan kasuwa da masu sayar da abubuwa iri iri suka kwana a bayan Urushalima.

21 Amma na tsauta musu, na ce, “Me ya sa kuka kwana a bayan garu? Idan kun ƙara yin haka zan kama ku.” Tun daga wannan lokaci ba su ƙara zuwa a ranar Asabar ba.

22 Sai kuma na umarci Lawiyawa su tsarkake kansu, su yi tsaron ƙofofin don a kiyaye ranar Asabar da tsarki.“Ya Allahna, ka tuna da wannan aiki nawa, ka rayar da ni saboda girman madawwamiyar ƙaunarka.”

23 A waɗannan kwanaki kuma na ga waɗansu Yahudawa waɗanda suka auro mata daga Ashdod, da Ammon, da Mowab.

24 Rabin 'ya'yansu suna magana da harshen Ashdod, ko wani harshe dabam, amma ba su iya yin magana da harshen Yahuza ba.

25 Sai na yi musu faɗa na la'ance su, na bugi waɗansu daga cikinsu, na ciccire gashin kansu, na sa su rantse da Allah, cewa ba za su aurar da 'ya'yansu mata ga 'ya'yan maza na bare ba, ko kuma su auro wa 'ya'yansu maza 'yan matan bare, ko su auro wa kansu.

26 Na faɗa musu cewa, “Ba a kan irin wannan ba ne Sulemanu Sarkin Isra'ila ya yi laifi? A al'ummai, ba sarki kamarsa. Allahnsa ya ƙaunace shi, ya sarautar da shi a Isra'ila, duk da haka baren mata suka sa shi ya yi zunubi.

27 Ba za mu yarda da abin da kuke yi ba, har mu aikata wannan mugunta ta rashin aminci ga Allahnmu, da za mu auro baren mata.”

28 Ɗaya daga cikin 'ya'yan Yoyada ɗan Eliyashib, babban firist, surukin Sanballat ne, Bahorone, saboda haka sai na kore shi daga wurina.

29 “Ka tuna da su, ya Allahna don sun ƙazantar da aikin firistoci da alkawarin zama firist da Lawiyawa.”

30 Da haka na tsarkake su daga kowane baƙon abu, na sa firistoci da Lawiyawa cikin aiki, kowa ya kama aikinsa.

31 Na kuma shirya yadda za a tara itace domin yin hadaya a kan kari, da kuma lokacin da za a kawo nunan fari.“Ya Allahna, ka tuna da ni, ka yi mini alheri.”

Surori

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13