1 Eliyashib, babban firist kuwa, tare da 'yan'uwansa firistoci, suka tashi suka gina Ƙofar Tumaki. Suka tsarkake ta, suka sa mata ƙyamarenta. Suka tsarkake garun zuwa Hasumiyar Ɗari da Hasumiyar Hananel.
2 Mutanen Yariko suka kama gini kusa da shi.Sai kuma Zakkur ɗan Imri ya kama gini kusa da na mutanen Yariko.
3 Iyalin Hassenaya suka gina Ƙofar Kifi, suka kafa katakanta, suka sa ƙyamarenta, da sandunan ƙarfe na kulle ƙofofinta.
4 Kusa da su kuma, sai Meremot ɗan Uriya, wato jīkan Hakkoz ya yi gyare-gyare.Kusa da shi kuma sai Meshullam ɗan Berikiya jikan Meshezabel ya yi gyare-gyare.Kusa da shi kuma sai Zadok ɗan Ba'ana ya yi gyare-gyare.