9 Sai muka yi addu'a ga Allahnmu, muka sa masu tsaro su yi mana tsaro dare da rana saboda su.
10 Mutanen Yahuza kuwa suka ce,“Ƙarfin ma'aikata yana kāsawa,Akwai komatsai da yawa da za a kwashe,Yaya za mu iya gina garun yau?”
11 Abokan gābanmu kuma suka ce, “Ba za su sani ba, ba kuwa za su gan mu ba, sai dai kawai su gan mu a cikinsu, za mu karkashe su, mu tsai da aikin.”
12 Da Yahudawan da suke zaune kusa da su suka zo, suka yi ta nanata mana irin shirin abokan gabanmu, wato za su zo su fāɗa mana.
13 Saboda haka na sa jama'a su ja ɗamara bisa ga iyalinsu a bayan garu, a wuraren da ba a gina ba. Suna riƙe da takuba, da māsu, da bakuna.
14 Da na ga mutane sun damu, sai na tashi na yi magana da shugabanni, da sauran jama'a, na ce, “Kada ku ji tsoro, ku tuna da Ubangiji mai iko, mai banrazana, ku yi yaƙi domin 'yan'uwanku, da 'ya'yanku mata da maza, da matanku, da gidajenku.”
15 Da abokan gābanmu suka ji mun san shirinsu, Ubangiji kuwa ya wargaje shirinsu, sai dukanmu muka koma wurin garun, kowa ya kama aikinsa.