1 Sa'ad da fa aka sanar da Sanballat, da Tobiya, da Geshem Balarabe, da sauran abokan gābanmu, cewa na gina garun, har ba sauran tsaguwa da ta ragu, ko da yake a lokacin ban riga na sa wa ƙofofi ƙyamare ba,
2 sai Sanballat da Geshem suka aika wurina cewa, “Ka zo mu sadu a wani ƙauye a filin Ono,” amma da nufin su cuce ni.
3 Sai na aika musu da manzanni, na ce, “Ina fama da babban aiki, ba ni da damar zuwa wurinku. Don me zan bar aiki in gangaro zuwa wurinku?”
4 Suka yi ta aiko mini da wannan saƙo har sau huɗu, ni kuwa na yi ta ba su amsa irin ta dā.
5 A karo na biyar sai Sanballat ya aiko da buɗaɗɗiyar wasiƙa ta hannun baransa, da irin maganar dā.