Neh 7:2-8-25 HAU

2 sai na ba ɗan'uwana, Hanani, da Hananiya, shugaban kagara, aikin riƙon Urushalima. Shi Hananiya mai aminci ne, mai tsoron Allah, fiye da sauran mutane.

3 Sa'an nan na ce musu, kada su buɗe ƙofofin Urushalima da sassafe, sai rana ta cira sosai, su kuma kulle ƙofofin da ƙarfe kafin matsara su tashi wajen faɗuwar rana. Su samo matsara daga mazaunan Urushalima, su sa su tsaye a muhimman wurare, waɗansunsu kuma suna zaga gidaje.

4 Birnin yana da faɗi da girma, amma mutanen da suke ciki kaɗan ne, ba a kuma gina gidaje ba tukuna.

5 Allahna kuwa ya sa a zuciyata in tara manya da shugabanni, da sauran jama'a don a rubuta su bisa ga asalinsu. Na sami littafin asali na waɗanda suka fara komowa. Ga abin da na tarar aka rubuta ciki.

6 Waɗannan su ne mutanen lardin Yahuza, waɗanda suka komo daga zaman talala da Nebukadnezzar Sarkin Babila ya kai mutane. Sun komo Urushalima da Yahuza. Kowa ya tafi garinsu.

7 Sun komo tare da Zarubabel, da Yeshuwa, da Nehemiya, da Seraiya, da Re'elaya, da Nahamani, da Mordekai, da Bilshan, da Misfar, da Bigwai, da Rehum, da Ba'ana.

8-25 Ga jerin iyalan Isra'ila da adadin waɗanda suka komo daga zaman doleiyalin Farosh, dubu biyu da ɗari da saba'in da biyu (2,172)iyalin Shefatiya, ɗari uku da saba'in da biyuiyalin Ara, ɗari shida da hamsin da biyuiyalin Fahat-mowab, wato zuriyar Yeshuwa da Yowab, dubu biyu da ɗari takwas da goma sha takwas (2,818)iyalin Elam, dubu da ɗari biyu da hamsin da huɗu (1,254)iyalin Zattu, ɗari takwas da arba'in da biyariyalin Zakkai, ɗari bakwai da sittiniyalin Bani, ɗari shida da arba'in da takwasiyalin Bebai, ɗari shida da ashirin da takwasiyalin Azgad, dubu biyu da ɗari uku da ashirin da biyu (2,322)iyalin Adonikam, ɗari shida da sittin da bakwaiiyalin Bigwai, dubu biyu da sittin da bakwai (2,067)iyalin Adin, ɗari shida da hamsin da biyariyalin Ater (na Hezekiya), tasa'in da takwasiyalin Hashum, ɗari uku da ashirin da takwasiyalin Bezai, ɗari uku da ashirin da huɗuiyalin Yora, ɗari da goma sha biyuiyalin Gibeyon, tasa'in da biyar