1 A rana ta ashirin da huɗu ga watan nan, sai jama'ar Isra'ila suka taru, suna azumi, suna saye da tufafin makoki, suna zuba toka a kansu.
2 Suka ware kansu daga bāre duka, suka tsaya, suna hurta laifofinsu da na kakanninsu.
3 Sa'ad da suke tsaye a inda suke, sai suka ɗauki kashi ɗaya daga cikin huɗu na yini, suna karanta littafin dokokin Ubangiji Allahnsu. Suka kuma ɗauki kashi ɗaya daga cikin huɗu ɗin na yinin, suna ta hurta laifofi suna kuma yi wa Ubangiji Allahnsu sujada.
4 Sai Yeshuwa, da Bani, da Kadmiyel, da Shebaniya, da Bunni, da Sherebiya, da Bani, da Kenani suka tsaya a kan dakalin Lawiyawa, suka ta da murya da ƙarfi ga Ubangiji Allahnsu.